SiyasaAfirka
China ta ce 'yan kasarta uku da aka sace a Ghana sun kubuta
April 1, 2025Talla
China ta ce 'yan kasarta uku da aka sace a kasar Ghana sun kubuta, to sai dai babu wani karin bayani da ta yi kan yadda aka yi garkuwa da su da yadda suka shaki iskar 'yanci, kamar yadda sanarwar ma'aikatar harkokin wajenta ta nunar.
Karin bayani:'Yan kasar China da aka yi garkuwa da su a Ghana na cikin koshin lafiya
Mai magana da yawun ma'aikatar Guo Jiakun ya ce suna ci gaba da aikin hadin gwiwa da mahukuntan Ghana don tabbatar da kare al'ummarta da ke zaune a kasar.
Jami'an tsaron Ghana sun sanar da fara bincike kan wasu da take zargin masu kai hari ne kan jiragen ruwa don sace mutane.
Karin bayani:Hulda tsakanin China da kasashen Afirka na kara karfafa
An dai sace mutane ukun ne lokacin da suke cikin jirgin ruwan Ghana suna kamun kifi.