China da Indonesia za su bunkasa tattalin arzikin Asiya
May 24, 2025China da Indonesia sun alkawarta yin aiki tare don bunkasa tattalin arzikin nahiyar Asiya tare da tabbatar da tsaro, kamar yadda firimiyar ChinaLi Qiang ya sanar a wannan Asabar bayan sauka a birnin Jakarta, don fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu.
Karin bayani:Girgizar kasa ta rusa gidaje sama da 100 a Indonesiya
Shugaban Indonesia Prabowo Subianto da kasarsa ke zama mafi karfin tattalin arziki a kasashen kudu maso gabashin Asiya, ya ce alakar Jakarta da Beijin za ta taimaka wajen bunkasa sha'anin cinikayya da kasuwanci, da kuma fasaha, wanda dama can suna da dadaddiyar mu'amala a tsakaninsu.
Karin bayani:China ta shirya inganta alaka da kasar Kanada
Kamfanin dillancin labaran China Xinhua ya rawaito cewa China ta tashi tsaye haikan wajen jaddada alaka da kasashen Asiya domin samawa kanta mafita mai bullewa, tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da laftawa kasashen duniya haraji mai nauyin gaske.