SiyasaLatin Amurka
China da Colombia sun cimma yarjejeniya
May 14, 2025Talla
Colombia ta bi sahun jerin kasashen kudancin Amurka da suka rattaba hannu kan shirin kawancen raya kasa da China. Wannan na zuwa ne bayan taron kolin shugabannin yankin da aka yi a Beijin.
Yarjejeniyar ta sami sahalewa bayan ganawa tsakanin shugaban China Xi Jingping da na Colombiya Gustavo Petro
Kashi biyu cikin kashi uku na kasashen kudancin Amurka sun sanya hannu a kan tsarin kawancen wanda zai bai wa Beijin karin tasiri ta fuskar siyasa da tattalin arziki tare da zuba jari kan muhimman ayyuka.
Yankin kudancin Amurka na kara zama wuri da ke daukar hankali yayin da Washington da Beijin suke fadada neman tasiri a siyasar duniya