SiyasaAsiya
Chaina, Iran da Rasha na taro kan makamashin nukiliyar Iran
March 14, 2025Talla
A makon da ya gabata ne dai shugaban Amurka Donald Trump ya aike da wasika ga jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei, inda ya bukaci hukumomin kasar da su shiga sabuwar yarjejeniyar nukiliya da Amurka ko kuma su fuskanci matakin soji. To amma da yake mayar da martani shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi watsi da bukatar Amurka, inda ya ce ba za su shiga duk wata yarjejeniya da Washington ba.
Karin bayani: Nukiliya: Iran ta ce babu ruwanta da Amirka
A shekara ta 2015, kasar Iran ta cimma yarjejeniyar nukiliya da kasashen Amurka da Rasha da Chaina da Burtaniya da Faransa har ma da nan Jamus domin a sassauta mata takunkumi. Amma 2018, gwamnatin Trump ta farko wa'adin mulki ta yi fatali da yarjejeniyar.
.