Chaina da Amurka za su gana kan batun kasuwanci
June 7, 2025Ma'aikatar harkokin wajen Chaina ta ce mataimakin Firimiya, He Lifeng zai kai ziyarar da tawagarsa bayan da Birtaniya ta aika masa da goron gayyata. Ana sa ran a yayin ziyarar, Lifeng zai yi tattaunawa ta farko kan batun tattalin arziki da kuma dabarun kasuwanci tsakanin China da Amurka.
Karin bayani: Amurka ta yi fito na fito da Chaina kan kudin haraji
A sakon da wallafa a shafinsa na Truth, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce wakilan Amurka a tattaunawar ta birnin Landan, za su samu jagorancin sakataren Baitil-malin kasar, Scott Bessent. A cewar Trump, tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan bayanan yarjejeniyar kasuwanci da aka kulla a watan Mayu tsakanin manyan kasashen biyu mafi karfin tattalin arziki. A takaddamar da ta barke kan kudin haraji, Shugaba Trump ya kara yawan harajin kudin fiton kan Chaina zuwa kaso 145 cikin 100, lamarin ya da sanya ita ma Chainar ta laftawa Amurka kudin haraji a matsayin ramuwar gayya.