Chadi ta dakatar da bayar da visa ga 'yan Amurka
June 8, 2025Shugaba Mahamat Idriss Deby ne ya sanar da matakin Chadi na dakatar da bayar da Visa ga 'yan Amurka da ke son shiga kasar. Hakan na zuwa ne a matsayin martani ga Amurkar da ta dakatar da bayar da izinin visa ga kasashe 12 ciki har da Chadi. Shugaba Donald Trump na Amurka ya zargi kasashen nahiyar Afirka da rashin yin cikakken tantacewa da ma kuma gazawarsu na mayar da mutane gida da suka wuce wa'adin izinin zamansu a Amurka.
Karin bayani: Donald Trump ya haramta wa 'yan kasashe 12 shiga Amurka
Matakin na Amurka da ake sa ran ya fara aiki a gobe Litinin ya hada da kasashen Afganistan da Myamar da Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango da Somaliya da Iran da Sudan da ma Yemen. Dama dai hana tafiye-tafiye na daga cikin mahimman manufofin wa'adin gwamnatin Trump na farko.