Kano: Cece-kuce kan killace yara almajirai
February 11, 2025Sai dai ana samun cece-kuce kan matakin gwamnatin Kanon da wasu ke ganin sa a matsayin matakin da bazai dore ba, idan aka yi la'akari da yawan yaran da suke yawo a jihar. Wasu dai na ganin, ana kashe kudin al'umma ba tare da duba abin da yafi cancanta ba. Wasu masana kuwa na bayyana cewar kamata ya yi, a fito da sahihiyar hanyar magance tushen da ya jefa yaran cikin wannan hali. Galibin yaran dai su kan yi hijira ne daga makwabtan jihohi, yayin da wasu kuma almajirai ne da ke guje wa makarantu su dawo kwana a kan tituna da karkashin gada.
To amma masu fashin baki kamar Kwamared Abubakar Ibrahim na ganin wannan matakin ba shi ya fi dacewa ba, idan aka yi la'akari da yadda ake ware makudan kudi wajen kula da yaran da a cewarsa alhakin hakan a kan iyayensu ya rataya. To amma a ra'ayin Safiyanu Husaini gwamnati ta yi kyakkyawan lissafi wajen killace yaran, domin rashin hakan ka iya haifar da matsalar tsaro a nan gaba. Da yawan yaran dai kanana ne da ba su wuce shekaru 10 zuwa 13 ba, wadanda suka fito daga jihohi makwabta har ma da Jamhuriyar Nijar. Wannan dai wata 'yar manuniya ce da ke kara nuna yadda wasu mutane, ke haifar 'ya'ya barkatai ba tare lissafin kula wa da su ba.