Jamhuriyar Nijar: Cece-kuce kan amfani Hausa
May 20, 2025A Jamhuriyar Nijar, a karon farko gwamnatin kasar ta fito ta yi ba bayani tare da karin haske kan dalilinta na zabar harshen Hausa daga cikin duk harsunan da ake magana da su a kasar a matsayin harshen a kasa da a nan gaba ka iya kasancewa harshen a aiki da ka iya cin wurin harshen Faransanci da kasar ta gada daga turawan mulkin mallaka na Faransa.
Karin Bayani: Hausa ya zama harshen kasa a Jamhuriyar Nijar
Tsawon kimanin mintuna sama da 40 ne dai Dokta Soumana Boubakar wanda shi ne Minista a fadar shugaban kasa Abdourahamane Tiani, kuma mai magana da yawun gwamnati, ya shafe a tattaunawar da aka yi da shi ta gidan talabijin na kasa na RTN, inda ya bayanii wanda ya kira da cewa a yi shi karara ta yadda kowa zai fahimta, ministan ya ce ya yi matukar mamaki kan yadda wasu 'yan kasar suka karkata manufar wannan mataki da aka dauka domin saka rudani a tsakanin 'yan kasa.
Da yake magana kan wannan batu Alhaji Baba Elmakiyya, shugaban kungiyar farar hula ta SEDEL/DH Niger, ya ce lalle shi ya fito ne daga kasbilar Sanwayawa, kua ya girma a yankin hassa, amma a ganin shi duk da cewa Hausa ita ce aka fi amfani da ita a Nijar da ya kyautu gwamnati ta ja da baya kan wannan batu.
Mutane da dama dai sun yi ta zargin magabatan kasar ta Nijar da nuna bangarannci wajen zaben harshen na Haussa a matsayin wanda aka fi amfani da shi a kasar wanda a cewar mai magana da yawun gwamnatin kasar kana ministan kula da fadar Shugaban kasa Dr Soumana Boubakar mutane su sani cewa babu komaia zuciyar shugaba Tiani sai kyaukyawar aniya ta yin aiki.
Shi dai wannan batu na harshen haussa batu ne da kasashe da ma manyan kungiyoyi irin su Tarayyar Afrika da ma cibiyar raya al'adu ta UNESCO suka aminta da shi. Sai dai abun jira a gani ko wannan fadakarwa za ta taimaka wajen kwantar da cece-kucen.