SiyasaJamus
CDU ta cimma yarjejeniyar kafa sabuwar gwamnati a Jamus
April 9, 2025Talla
Jam'iyyar CDU mai ra'ayin rikau ta cimma matsayar kafa sabuwar gwamnati da jam'iyyar Social Democratic Party (SPD) a nan Jamus bayan babban zaben kasar da aka gudanar a watan Fabrairun 2025.
Karin bayani:An kama hanyar kafa gwamnatin hadaka a Jamus
CDU da SPD sun cimma yarjejeniyar ce bayan shafe makonni suna tattaunawa wajen fitar da jadawalin kafa sabuwar gwamnati tun bayan nasarar da Friedrich Merz na Christian Democrats (CDU) ya samu a matsayin sabon shugaban gwamnatin Jamus mai jiran gado.
Karin bayani:Zaben Jamus: Yan takara sun tafka muhawara
Nan gaba kadan ake sa ran fitar da taswirar kafa sabuwar gwamnatin Jamus.