CDU da SPD za su koma tattaunawa don kafa gwamnati a Jamus
March 3, 2025A ranar Litinin ne bangaren jagoran jam'iyyar CDU Friedrich Merz da kuma na shugabannin jam'iyyar SPD za su koma teburin tattaunawa domin duba yiwuwar samar da hadaka ta sabuwar gwamnatin Jamus.
A ranar Juma'a ce aka fara tattaunawar tsakanin bangarorin biyu kuma a yanzu an koma tattaunawar ce da gaggawa bayan cacar baka da ta kaure tsakanin shuagban Amurka Donald Trump da kuma na Ukraine Volodymyr Zelensky a fadar White House a ranar Juma'a.
Ya ya kawancen kafa gwamnatin Jamus zai kasance?
Lamarin da ya faru ya sa wasu kasashen Turai fara ganin Amurka a matsayin kasar da babu tabbbas kanta a kan sha'anin kawancen tsaro.
Bayan nasarar da ta samu, jam'iyyar CDU/CSU na neman yadda jagoranta Friedrich Merz zai maye gurbin Olaf Scholz a matsayin sabon shugaban gwamnatin Jamus.
Jam'iyyar CDU/CSU na kan gaba a zaben Jamus
Jam'iyyar ta Scholz SPD ita ce ta zo ta uku bayan CDU da AfD sun zo a matsayin ta daya da ta biyu.