CDU/CSU da SPD za su sanya hannu kan jadawalin mulkar Jamus
April 28, 2025A wannan Litinin jam'iyyun CDU da SPD za su sanya hannu kan yarjejeniyar da suka cimma game da jadawalin gudanar da mulki, bayan shafe tsawon makonni suna tattaunawa, a daidai lokacin da ya rage kwanaki kadan a tabbatar da jagoran CDU Friedrich Merz a matsayin shugaban gwamnatin Jamus.
Karin bayani:CDU ta cimma yarjejeniyar kafa sabuwar gwamnati a Jamus
Nan gaba a Litinin CDU za ta gudanar da taron jam'iyya a Berlin babban birnin kasar, inda Friedrich Merz zai gabatar da sunayen ministocin gwamnatinsa, yayin da abokiyar kawancenta CSU za ta yi na ta taron a birnin Munich domin fitar da na ta ministocin.
Karin bayani:An kama hanyar kafa gwamnatin hadaka a Jamus
Bisa yarjejeniyar da aka cimma, CDU da SPD za su gabatar da sunayen ministoci bakwai-bakwai, yayin da aka ware wa CSU gurabe uku na ministocin.
Ana sa ran tabbatar da Mr Merz a matsayin shugaban gwamnatin Jamus a ranar 6 ga watan Mayu mai kamawa.