Najeriya: Karin harajin cirar kudi a ATM
February 12, 2025Kama daga zare tallafin man fetur ya zuwa karin kudin wuta dama ku din waya ta salula dai, miliyoyin al'ummar Tarayyar Najeriyar suna ji a jiki sakamakon manufofin kudi na gwamnatin kasar. To sai dai kuma wani sabon karin kaso 285 kan harajin ciro kudi ta akwatin kudi na bankuna ne, ke neman yamutsa hazo a Najeriyar a halin yanzu. Babban bankin kasar CBN dai ya ce, daga farkon watan gobe na Maris harajin zai tashi daga Naira 35 zuwa naira 100 kan kowane naira dubu 20 da aka zara ta akwatin ATM. Haka kuma adadin yana shirin kai wa har kusan Naira 500, in har akwatin na ajiye a shaguna da ragowar cibiyoyin hada-hadar kudi da ke a wajen banki. Wannan ne dai karo na farko, cikin sehakaru shida da babban bankin ke kara harajin zarar kudi a cikin akwatin banki. Ana dai kallon sabon matakin ka iya tasiri, ga kokarin inganta kanana na sana'o'in da ke dogaro da takarda wajen hada-hada.
A shekara ta 2019 ne dai, Najeriyar ta rage harajin daga Naira 65 zuwa 35 da nufin rage radadi kan talakawan da ke zaman na kan gaba cikin hada-hadar kudi na takarda. To sai dai kuma ko a tsakani na kwarraru ga tattalin arzikin, sabon matakin na janyo muhawara mai zafi cikin kasar a halin yanzu. Kara harajin cire kudin a tunanin Dakta Hamisu Ya'u da ke zaman kwarrare ga tattalin arziki, na iya shafar shirin kudin na zamani da ke dada bunkasa cikin kasar a halin yanzu. A watanni shida na farkon shekarar da ta shude dai, an yi hada-hadar kudi ta ATM da POS a Najeriyar da yawansu ya kai kusan NairatTriliyan 100 a watanni shida na farkon baran kadai. Yusha'u Aliyu dai na zaman tsohon ma'aikacin banki a kasar, kuma ya ce karin ya wuce tunani da hankali. A shekarar 1989 ne dai, Najeriyar ta kaddamar da tsarin ATM a kokarin mayar da harkar bankin zuwa ta zamani.