Carney ya ci zaben firaministan Canada da zai kafa gwamnati
April 29, 2025Jam'iyyar Liberal ta Firaministan Canada Mark Carney mai sassaucin ra'ayi ta samu nasarar lashe zaben da zai ba ta damar kafa gwamnati, bayan da al'ummar kasar suka amince cewa Carney zai iya kalubalantar manufofin shugaban Amurka Donald Trump.
Karin bayani:Indiya da Canada sun sallami jakadun kasashen biyu
Mr Carney mai shekaru 60, wanda ya maye gurbin firaminista Justin Trudeau a cikin watan Maris da ya gabata, ya taba rike mukamin gwamnan babban bankin Canada da kuma na kasar Burtaniya, kuma yakin neman zabensa ya mayar da hankali wajen fadada komar tattalin arzikin kasar, domin rage dogaro da Amurka, har ma da kalubalantar manufofin shugaba Trump.
Karin bayani:Trump ya sha alwashin karin kaso 50 na haraji kan Kanada
Jagoran jam'iyyar 'yan ra'ayin rikau ta Conservative Pierre Poilievre ya gaza samun kuri'un da za su ba shi damar zama firaminista, to sai dai ya samu rinjayen kafa jagorancin adawa mai karfi.
A jawabin da ya gabatar jim kadan bayan sanar da nasarar, Mr Carney ya ce kasarsa ba za ta taba mantawa da cin amanar da Amurka ta yi mata ba, kuma za su yi nasarar yakin kasuwanci a tsakaninsu.