Canada za ta goyi bayan kafa kasar Falasdinu
July 31, 2025Matakin na zuwa ne bayan da Burtaniya da Faransa suka cimma wannan matakin da suka bayyana a matsayin hanya daya tilo da za ta kawo karshen rikicin dake tsakanin Isra'ila da Hamas.
Firaminista Mark Carney ya ce, za a cimma yarjejeniyar gyara daga bangaren hukumomin Falasdinu da suka shafi amincewa da tsarin dimukuradiyya da cire Hamas a harkar zabe.
Amurka wacce ta yi tir da matakin na baya-bayan nan daga Canada, Shugaba Doland Trump ya ce zai iya shafar yarjejeniyar kasuwanci da za su cimma.
Goyon bayan kasashen na samar da kasar Falasdinu mai cin gashin kai, na zuwa ne bayan gaza shawo kan Isra'ila ta dakatar yaki a Gaza.
Rahotannin baya-bayan nan sun tabbatar da mutuwar akalla Falasdinawa 30 wadanda sojojin Isra'ila suka budewa wuta yayin da suke jiran agajin abinci.
Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta ce kwanaki hudu na tsagita bude wuta da Isra'ila ta yi a Gaza, har yanzu mutane na mutuwa saboda yunwa da rashin abinci mai gina jiki.