Canada na zaben gwamnati da za ta tabbatar da makomar kasar
April 28, 2025Da farko dai alamu sun yi nuni da cewar jam'iyyar masu sassaucin ra'ayi karkashin sabon Firayiminista Mark Carney na shirin shan kaye, a hannun 'yan jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya ta Pierre Poilievre, amma godiya ga barazanar shugaban Amurka a kan kasar, wadda ta sauya alkiblar siyasa da ma hasashen makomar zaben.
Carney, mai shekaru 60, bai taba rike wani mukami na siyasa ba, amma ya maye gurbin Justin Trudeau a matsayin firayiminista a watan Maris da ya gabata. A baya ya yi aiki a matsayin ma'aikacin bankin a fannin saka hannun jari kafin ya zama gwamnan babban bankin kasar Canada da Birtaniya.
Ya ce kwarewarsa ta fuskar kudi ta shirya shi don jagorantar martanin Canada game da harajin Trump. Ya kuma yi alkawarin farfado da kasuwancin cikin gida da fadada damar tattalin arzikin Canada a kasashen waje, don yanke dogaro da Amurka.