SiyasaSudan ta Kudu
Sudan ta Kudu: Cafke minstan man fetur
March 5, 2025Talla
Mai magana da yawun Riek Machar da ke zman mataimakin shugban ksa na farko a Sudan ta Kudu Puok Both Baluang ne ya sanar da hakan, inda ya ce an cafke ministan albarkatun man fetur din kasar Puot Kang Chol da mataimakin shugaban rundunar sojoji. Haka kuma ya sanar dacewa, an sanya duka manyan sojojin da ke goyon bayan Marchar karkashin daurin ta-la-la. Tun a shekara ta 2018 ne aka cimma sulhu a Sudan ta Kudu, abin da ya kawo karshen rikicin shekaru biyar a hukumance tsakanin shugaban kasar Salva Kiir da mataimakinsa na daya wato Machar. Rikicin dai ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da tilasta wasu da dama gudun hijira. Sai dai har kawo yanzu, mutanen biyu da ke shugabancin Sudan ta Kudu na yi wa juna kallon hadarin kaji.