Buƙatar ƙara jarukan bankunan Turai
October 5, 2011Hukumar zartawar Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce ƙasashen mambobin ƙungiyar sun daideta kan buƙatar haɗa ƙarfi da ƙarfe a wuri ɗaya domin sake zuba jari a bankunansu domin kauce wa yaɗuwar matsalar bashi. Kantomar harkokin tattalin arziƙin ƙungiyar, Olli Rein ya faɗa wa jaridar Financial Times cewa ana buƙatar ƙara jarukan bankunan ƙasashen Turai domin kauce wa matsalar kuɗi da kuma kau da halin rashin tabbas. Hakan ya zo ne a daiden lokacin da ƙasashen Faransa da Beljiyam suka ƙara ƙaimi wajen ɗaukar matakan ceto bankinsu na haɗin-gwiwa wato Dexia da ke kula da zuba kuɗi a harkokin gwamnatocin Turai. Matsalar bashin da ke addabar Girka na shafan bankin na Dexia wanda hannayen jarinsa suka ragu da kashi 37 daga cikin dari da safiyar 04.10.2011 ko kafin a tabbatar da taɓarɓarewarsa.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman