Burtaniya za ta biya mutanen Kenya diyyar kudade masu yawa
August 22, 2025Burtaniya ta amince da biyan diyya ga mazauna wani yankin Kenya da gobara ta tashi yayin atisayen sojoji. Gobarar ta tashi ne a watan Maris na shekarar 2021 a kauyen Lolldaiga, kusa da sansanin horon sojojin Burtaniya da ke Nanyuki, arewacin Kenya.
Mazauna yankin sun zargi sojojin Burtaniya da ke atisaye a yankin da haddasa gobarar da ta cinye yawancin dajin, tare da barin wasu abubuwan fashewa da suka jikkata jama'a.
Karin bayani: Zimbabuwe: Diyya ga manoma farar fata
Daga baya wani soja dan Birtaniya ya wallafa a shafukan sada zumunta, yana mai ikirarin daukar alhakin haddasa gobarar, lamarin da ya sa Jakadiyar Birtaniya a lokacin ta bayyana bacin ranta tare da alkawarin binciken rundunar sojojin kasarta.
Gwamnatin Birtaniya a wannan Juma'a ta bayyana rashin jin dadinta bisa faruwar lamarin.