'Akwai dama mai kyau ta kawo karshen yakin Ukraine'
August 13, 2025Firaministan Burtaniya Keir Starmer ya ce akwai dama mai kyau ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Ukraine bisa shiga tsakanin shugaban Amurka Donald Trump, wanda zai yi ganawar keke da keke da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a ranar Juma'a mai zuwa a Alaska.
Keir Starmer ya ce: ''A cikin shekaru kusan uku da rabi da fara wannan rikici ba mu taba kusantar samun mafita ta hakika ba domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Amma a yanzu muna ganin haske sakamakon aiki tukuru da shugaba Amurka Donald Trump ke yi.''
A daidai wannan lokaci shugaban kasar Ukraine Vlodymyr Zeklensky ya nanata cewa batun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta nan take shi ne kamata ya zama jigo a ganawar da Trump da Putin za su yi, sannan kuma ya bukaci a kara labta wa Rasha takunkumai muddin ta ki amincewa.
A cikin wannan yanayi dai fadar mulki ta Kyiv da kasashen Turai na fargabar a cimma yarjejeniya a tsakanin shugabannin Amurka da na Rasha a ranar Juma'a da ke tafe ba tare da an yi la'akari da muradun Ukraine ba.