Burkina Faso ta dakatar da ayyukan kungiyoyin ketare
July 6, 2025Talla
Burkina Faso ta soke lasisin wasu kungiyoyi hudu na kasashen waje wadanda ke aiki a kasar da ke karkashin mulkin soji, tare da dakatar da wasu karin kungiyoyi biyu.
Wannan labari dai ya fito ne daga wata takardar dokokin da aka gani a cewar kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.
Dokokin da aka sanya a tsakiyar watan Yuni sun ambaci wani minista a gwamnatin ta Burkina Faso wanda ya bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne saboda rashin bin ka'idojin aiki da suka shafi kungiyoyin hudu.
Shugaban Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traore wanda ya karbi iko da tsinin bindiga a watan Satumba 2022, ya sanya dawo da ikon kasa a hannun gwamnati a matsayin guda daga cikin manyan manufofinsa.