Burkina Faso ta ce ta dakile yunkurin juyin mulki
April 22, 2025Talla
Gwamnatin ta ce an shirya makarkashiyar juyin mulkin ne a kasar Ivory Coast. Gwamnatin mulkin sojin ta sanar da cewa ta dakile yunkurin juyin mulkin wanda aka kitsa domin haifar da rudani a kasar ta yammacin Afirka.
Ta ce an gano wadanda suka shirya juyin mulkin daga makwabciyarta Ivory Coast.
Shugaban gwamnatin rikon kwarya Ibrahim Traore Kaptin din soja wanda shi kansa ya hau shugabanci ne ta hanyar juyin mulki a 2022 ya sha zargin kasar Ivory Coast da bai wa masu adawa da shi mafaka.