Bulgaria za ta fara amfani da kudin Euro
June 4, 2025A rahoton karshe da ta gabatar, wata hukuma da aka nada ta ce bayan rage hauhawar farashin kayayyaki, Bulgaria ta cika dukkan sharudda na zama kasa ta 21 a Tarayyar Turai da za ta yiamfani da kudin na gama gari.
Shugabar Hukumar gudanarwar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, ta ce godiya ga Euro tattalin arzikin Bulgaria zai kara karfi, tare da kara habaka ciniki da abokan hadin gwiwar yankin da ke amfani da da tsarin Euro da saka hannun jari kai tsaye a waje, damar samun kudi, kazalika ingantattun ayyuka da kuma samun kudin shiga na gaske.
Bulgaria ta kasance memba a EU tun shekarar 2007, kuma tun a 2024 ta fara shirin maye gurbin kudinta na kasa wato lev da kudin Euro, amma faduwar darajar kudin kasar da ya haifar da hauhawar farashin kaya da kusan kaso 10 cikin 100, ya sa a ka dage batun a lokacin.