Bukukuwan Ista a cikin kalubalen tsaro a Najeriya
April 17, 2022
Bikin Isata lokaci ne da mabiya addinin kirista ke gudanar da hidimomi na ibada, inda wasu kan yi azimi na kwanaki 40, kafin a bisani su karkare da sallar Ista. Sai dai a wannan karo matsalar tsaro ta janyo komabaya ga mabiya a yankuna da ke fama da hare-haren 'yan bindiga.
Christopher Iza Ziraci Turakin Irigwe. wanda ke zama basaraken gargajiya a Bassa, ya ce: "Kafin yanzu muna bikin Ista muna jin dadi, saboda mutuwa da tashin Yesu. Amma a wannan karon muna bikin da tsoro, ba kamar da ba. A baya za ka ga ana biki ana jin dadi ana walwala, ana komai da komai, amma a yanzu ya zama abin tsoro, musamman a Bassa. "
Mujami'u a cikin jos da kewaye sun gudanar da bikin na Ista cikin kwanciyar hankali. Elder Michael Cha, wani shugaba a mujami'ar ECWA ya ce: " Mun je mun yi adu'o'i lafiya, koda yake a cikin tsoro ne. Allah sa mu yi komai mu kammala lafiya."
A gabanin bikin na Ista ne aka kai wani mummunan hari a Kanem da ke tsakiyar jihar Filato, inda aka yi asarar rayukaa da dukiyoyi. Mrs Lydia Hassan ta ce: " Ista a wurin mu a wannan shekara bai yi kyau ba. Mutane kadan ne suka je mujami'u suka yi adu'o'i saboda suna tsoro. Dama hakuri ake yi, abinci ma da kyar ake samu ga tsadar rayuwa, ga shi kuma yanzu an kone gidaje. "
Anyi bikin Ista a bana cikin matakan tsaro a jihar Filato, musamman a yankunan da ake fama da hare haren 'yan bindiga, Wasu mazauna kauyuka sun ce suna iya ganin jami'an tsaro daidai gwargwado a yanzu ba kamar yadda yake a kwanakin baya ba.