Bukatar taron gaggawa a kan Gaza
August 8, 2025Talla
Kasashe da dama sun bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da taron gaggawa a kan matakin Isra'ila na shirin karbe iko da yankin Zirin Gaza na Falasdinu da yaki ya ɗaiɗaita. Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa, wasu majiyoyi guda biyu na diplomasiyya sun bayyana masa akwai kasashe da dama da ke neman a gudanr da taron gaggawar kan shirin Isra'ila na mamaye Zirin Gaza.
Karin bayani: Mai zai faru bayan Isra'ila ta mamaye Gaza?
Shi ma jakadan Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansour ya shaidawa manema labarai cewa, a yanzu akwai kasashe da dama da suka bukaci zaman gaggawar a madadin Falasdinu da kuma kasashensu.