Buhari ya nada sabon Sifeto Janar na 'yan sanda
April 6, 2021Talla
Minista a ma'aikatar da ke kula da 'yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi ya ce sabon Sifeto Janar din mai suna Usman Alkal zai kama aiki nan take, sai dai kuma nadin na zuwa ne cikin yanayin maras kyau na tsaro dama makomar 'yan sandan.
Ko a farkon wannan mako sai da aka kai hari a hedikwatar yan sanda da ke birnin Oweri hedikwatar jihar Imo a Kudancin kasar.
Ministan ya kara da cewa kalubalen tsaron ne suka kai ga sabon sauyin da ake sa ran zai yi tasiri a tarrayar ta Najeriya.