'Yan majalisa a Nijar na son tsige Rafini
June 28, 2019'Yan majalisar dokoki na bangaren masu mulki sun ce matakin 'yan adawar bai saba doka ba, domin haka tsarin dimukuradiyya ya tanada. Sai dai sun ce zargin 'yan adawar ba shi da tushe, kuma da wuya hakarsu ta cimma ruwa.
Korone Masani, dan majalisar dokokin Nijar na bangaren adawa, yace "Mu 35 muka cike takarda muka ajiye, kuma mun dauka cewa mu din ne za mu fito a cikin kuri'a. Ko da ya ke dama mun san abin da zai faru da 'yan amshin shata kuma gashi an gani."
A farkon wannan makon ne 'yan majalisar dokoki na bangaren jam'iyyun adawa suka shigar da takardar neman tsige gwmnatin firaminista Brigi Rafini a gaban shugaban majalisar dokokin kasar. 'Yan majalisar adawar na zargin gwamnatin ta Rafini da gazawa wajen shawo kan matsalolin da suka mamaye kasar.