BRICS na tsara tunkarar manufofin shugaban Amurka Trump
April 28, 2025Kungiyar raya tattalin arzikin kasashe ta BRICS za ta yi taro na musamman a wannan Litinin a kasar Brazil, da nufin cimma matsaya guda daya wajen tunkarar barazanzar sabbin manufofin tattalin arzikin shugaban Amurka Donald Trump, wadanda suka hargitsa sha'anin kasuwancin duniya.
Karin bayani:Putin ya karbi shugabanni a taron kolin BRICS
Taron na zuwa ne a daidai gabar da asusun ba da lamuni na duniya IMF ke sanar da zaftarewar bunkasar tattalin arzikin kasashen duniya, musamman Amurka da China, sanadiyyar sabon tsarin karin harajin da Mr Trump ya laftawa kasashe.
Ministan harkokin wajen Brazil Mauro Vieira ne zai kaddamar da bude taron, wanda zai samu halartar takwarorinsa na Rasha Sergei Lavrov da na China Wang Yi da sauransu.
karin bayani:Ana shirin bude taron kasashen BRICS a Rasha
Shugabannin kasashen Brazil da Rasha da India da China, da kuma na Afirka ta Kudu za su yi taro na kwanaki biyu a birnin Rio de Janeiro, domin share fagen babban taron da kungiyar ta BRICS za ta gudanar a cikin watan Yuli mai zuwa.