SiyasaArewacin Amurka
Brazil za ta gurfanar da Isra'ila ICC kan 'kisan kiyashi'
July 24, 2025Talla
Ma'aikatar harkokin wajen Brazil ta sanar da cewa ta kammala tattara alkalumanta na gurfanar da Isra'ila a kotun birnin Haque kamar yadda kasashen Colombiya da Libya da kuma Mexico har ma da sauran kasashe za su gurfanar da Isra'ilan. Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya jaddada matsayarsa kan abin da Isra'ila ke aikata wa a Gaza a matsayin 'kisan kiyashi'.
Karin bayani:Kotun ICC ta bada sammacin kama Netenyahu da jagororin Hamas
A watan Disambar 2023, kasar Afirka ta Kudu ta shigar da kara kotun duniya kan zargin Isra'ila da kisan kare dangi wanda kuma ya ci karo da yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya na 1948, wanda ya kare duk wani bil Adama daga kisan kiyashi.