Birtaniya za ta amince da kasar Falasdinu
July 29, 2025Talla
Yunkurin da zai yi tasiri, wani bangare na shirin "zaman lafiya mai dorewa" da Starmer ke gabatarwa, ya zo ne bayan da shugaban na Burtaniya ya kira majalisar ministocinsa daga hutu cikin gaggawa don tattaunawa kan tabarbarewar al'amura a yankin da ke cikin talala.
Firaminista Keir Starmer ya jadda da cewa babu bambanci tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas, bukatar Birtaniya ga Hamas na sakin dukkan wadanda suke garkuwa da su yana nan, sannan su amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da cire hannu a gwamnatin Gaza.
Wannan na zuwa ne bayan da Shuagabn Faransa Emmanuel Macron ya sanar a makon jiya cewa, zai amince da kasar Faladsinu a hukumance a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a watan Satumba.