Birnin Bambari ya fada hannun 'yan tawaye
December 22, 2020Jami'an gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da na Majalisar Dinkin Duniya da kuma magajin garin Bambari suka ce an yi musayar wuta na sa'o'i biyu tsakanin 'yan tawayen da sojojin kiyaye zaman lafiya na Minusca kafin birnin da ke zama na hudu a girma a kasar ya fada hannu 'yan bindiga. Dama tun da sayin safiyar ranar talata ne fada ya sake barkewa a garin na Bambari tsakanin masu dauke da makamai ta UPC da sojojin gwamnati.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Rasha ta sanar da cewa ta tura da kari sojoji 300 zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, domin taimaka wa gwamnatin kasar tinkarar farmaki da kungiyoyin ‘yan tawaye suka kai wanda ta danganta da yunkurin juyin mulki. Ita Rasha ta nuna damuwa matuka game da rikicin siyasa da na tawaye da ke faruwa a 'yan kwanakin da suka gabata, gabanin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa.