Biranen Afirka mafiya tsadar rayuwa
Kudaden haya, abinci da kuma nishadi: Ina wuraren da ake samun tsadar kayayyaki? Kowace shekara ana gudanar da binciken birane 200 na duniya da aka fi tsadar rayuwa. Biranen Afirka na kan gaba wajen tsadar rayuwa.
Matsayi na 10: Abuja
Haya, abinci da nishadi: Waje ne da ake samun ma'aikata daga kasashe da kamfanoni suke bukatar zuwa. Duk shekara bincike ya nuna daga cikin birane 200 da ke kan gaba wajen tsadar rayuwa. Abuja babban birnin Najeriya ya kasance a matsayi na 10: An taba cewa Nelson Mandela da ya kai ziyara birnin ya tambaya "Ina za mu je ga Turai-nan abin da aka gani haka yake."
Matsayi na 9: Conakry
Bincike kan abubuwa 200 da kudaden ayyuka, misali kudaden haya, da motocin safa, da abinci, da kayayyakin sakawa, da kuma nishadi. Conakry babban birnin kasar Gini ya kasance a sahun gaba wajen tsadar kayayyakin bukatun rayuwa, abin da ya sa birnin kasancewa daga cikin mafi yawan tsadar rayuwa a Afirka.
Matsayi na 8: Bamako
Kusan mutane milyan biyu ke zama a babban birnin na Mali. Akwai matsaloli na lamuran jinkai sannan kasar ba ta da iyaka da teku, sai dai akwai kamfanoni da kungiyoyin agaji na kasashen ketare. Akwai matsalolin samun ingantattun gidajen haya, ga tashin farashi. Sannan ana matsa wa baki wajen biyan kudaden haya da aka tsauwala musu kudi.
Matsayi na 7: Brazzaville
Waje mai matukar ban sha'awa da ke zama babban birnin Jamhuriyar Kongo, wanda ya fuskanci yakin basasa daga 1997 zuwa 1999 ya zama mai tasiri. Farashin kayayyaki a Brazzaville ya zama mai tsada sosai: Kwalabar Coca-Cola daya ta kai na guda hudu a Dubai.
Matsayi na 6: Lagos
Lagos ke zama cibiyar kasuwancin Najeriya wanda ke bunkasa kullum, birnin ya kunshi talakawa kamar yadda akwai masu tsananin arziki. Mafi yawan masu hannu da shuni suna rayuwa a tsibirin birnin. "Akwai dubban ma'aikata da ke tururuwa zuwa aiki. Mutum zai kwashe sa'o'i hudu kan tafiyar kilomita 35" a cewar wakilin DW Adrian Kriesch. A wajensa rayuwa a Lagos tana da tsada kamar rayuwa a Jamus.
Matsayi 5: Kinshasa
Babban birnin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo yana dauke da mutane fiye da miliyan tara inda yake bin birnin Lagos wajen yawan mutane a Afirka. Akwai gidaje na kasaita a wata unguwa da ke kusa da kogin Kongo. "Saboda yawan yakin da ke gocewa a kasar tilas 'yan kasashen ketare suke daukan matakan kariya." A cewar wakilin DW Philipp Sandner, wanda ya yi rayuwa ta shekara guda a Kongo.
Matsayi 4: Libreville
Kasar da ke tsakiyar Afirka ta Gabon ta kunshi kimanin mutane milyan guda, tanada arziki yayin da 'yan kasashen ketare ke samun ribar aikin da suke yi. Haka lamarin yake a Libreville babban birnin kasar da ke jan hankalin mutane. Misali akwai tsadar shiga gidajen rawa.
Matsayi na 3: Victoria
Babban birnin tsibirin Seychelles yana samun bunkasa tun lokacin da Turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka kafa gudanar da harkokin mulkin tsibirin. Mai yiwuwa shi yasa Yerima William na Birtaniya da matarsa Kate suka yi zaman angonci a tsibirin. Ana biyan kusan dalar Amirka 5000 na kwana guda a gidajen da suke kusa da wajen shakatawa na bakin teku.
Matsayi na 2: N'Djamena
Birnin mafi tsadar rayuwa na duniya a kasashe masu fama da talauci? Sannu da zuwa Cadi, a tsakiyar Sahara. A nan babu tashar jiragen ruwa, babu hanyoyin jiragen kasa, babu wasu ingantattun hanyoyi. "Duk abin da 'yan kasashe ketare za su saya a N'Djamena, tilas ta jiragen sama suke zuwa." A cewar wakilin DW Tim Jánszky, wanda ya dade yana rayuwa a Cadi.
Matsayi na 1: Luanda
Babban birnin kasar ta Angola ba wai a kasashen Afirka kawai ya fi kowane birni tsadar rayuwa ba, amma a duniya baki daya. Angola tana cikin kasashen Afirka da ke kan gaba wajen fitar da man fetur. Tun bayan kawo karshen yakin basasa a shekara ta 2002 ake samun kwararar ma'aikata zuwa birnin Luanda. Akwai karancin gidajen kwana, kuma gidaje masu inganci suna kai Euro 10,000 zuwa 35,000 a wata.
Rayuwar tana gargada
Farashin kaya a Luanda babban birnin Angola ya kasance abin da ya wuce tunani, mafi yawan mutane suna unguwannin talakawa. Babu tsayayyar wutar lantarki da ruwan sha. Shekaru da aka kwashe ana samun bunkasar tattalin arziki sakamakon fitar da man fetur bai kai ga talakawan kasar ba. Akwai tazara tsakanin talakawa da masu arziki. Irirn wannan matsala ake gani a mafi yawan biranen Afirka.