Bikin ranar sake hadewar Jamus
October 3, 2012Shekaru 22 tun da aka sake samun hadewar kasar Jamus, akwai alamun cewar gibi tsakanin yankin yammaci da gabashin kasar yana kara fadada. Yanzu haka, tattalin arzikin yankin gabashin Jamus yana samun koma baya, inda bai wuce misalin kashi 71 cikin dari na karfin tattalin arzikin yammacin kasar ba. Matasa suna ci gaba da kauracewa yankin, saboda rashin ganin alamun haske ga rayuwarsu, musamman sakamakon karancin wuraren aikin yi ko samun horo. Hakan ya sanya masana su kai ga fahimtar cewar bayan dokin da aka nuna game da hadewra kasar ta Jamus, samun nasarar daidaita rayuwa tsakanin yankunan biyu ba zai zama abu mai sauki ba. .
Misalin shekaru 41 bayan zaman rarrabuwa tsakanin yankin yammmaci da gabashin Jamus, ya zama tilas wadannan yankuna biyu su kafa sabon tushe na daidaita rayuwa tsakanin su,bayan da mazauna yankin gabashin Jamus suka sami nasarar gwagwarmaya kan shugabannin su na danniya, suka kuma zabi zama cikin yanci da walwala. Tun kafin hakan kuwa sai da majalisar dokokin Jamus ta gabas ranar 23 ga watan Agusta na shekara ta 1990, ta amince a shigar da yankin na gabas cikin taraiyar Jamus da kuma karbar tsarin mulkin kasar ta Jamus, karkashin fanni na 23 na kundin tsarin mulkin. Sakamakon wannan nasara, kasar ta Jamus ta sake hadewa ranar ukku ga watan Oktoba na shekara ta 1990. Lokacin bukukuwan wannan rana a birnin Munich, Pirimiyan jihar Bavaria, Horst Seehofer, wanda kuma shine shugaban babbar majalisar dokoki wato Bundesrat mai ci, ya tunatar da kwazon da mazauna Jamus ta gabas suka nuna, abin da ya zama tushe sake hadewar kasar.
Tun da farko sai da mazauna yankin gabashin Jamus suka tashi tsaye ne bisa adawa da shugabannin su, sa'annan aka share hanyar da ta kai ga sake hadewarmu cikin yanci, kuma babu shakka godiya mai yawa ga wadannan mutane, saboda kwazon da suka nuna.
Ta fannin siyasa da rayuwa da zamantakewa, kamar yadda tsohon shugaban gwamnatin Jamus, Willy Brandt ya taba fadi, mutanen da suke dama can tare suke, su sake samun damar hadewa su bunkasa tare. Jim kadan bayan da yankunan biyu suka hade, an kaddamar da wani gagarumin asusu na sake gina yankin gabashin kasar, inda tsakanin shekara ta 1990 zuwa shekara ta 2010 aka zuba masa kudi misalin Euro miliyan dubu har sau dubu daya da dari hudu da aka yi amfani dashi domin aiyukan sake gina gabashin na Jamus.
Rushe katangar da ta raba birnin Berlin gida biyu, wadda kuma a hakika ta kawo raba nahiyar Turai, ya taimaka ba ma game da sake hadewar Jamus bane, amma har ya sake karfafa hadin kai a nahyiar Turai. Kakakin majalisar dokokin Jamus ta Bundestag, Nobert Lammert dake jawabi a wurin bikin ranar ta hadin kan Jamus ya nunar da muhimancin wannan hadin kai.
Al'amarin da shine mafi kawo farin ciki a tarihin Jamus bayan yaki, wato faduwar katangar Berlin, ya kuma zama mai muhimanci a al'amuran nahiyar Turai baki daya. Inda ba tare da an kawo karshen rarrabuwar nahiyar Turai ba, da kuwa sake hadewar Jamus bai yiwu ba. A daya hannun kuma, sake hadewar kasamu, shine sharadin hadin kai da bunkasar nahiyar Turai da karfafa dangantaka tsakanin kasashen yammacin da gabashin Turai. Godiya ta musamman ga makwabtanmu da abokanmu na ketare da kawayenmu, wadanda inda ba tare dasu ba, da bamu sami damar bikin kewayowar ranar hadewar Jamus ba.
Kakakin na majalisar dokoki yace nasarorin da aka samu na bunkasar gabashi da yammacin Jamus tare, wani sako ne ga nahiyar Turai, saboda Jamus da Turai duka jirgi daya ya kwasosu, saboda muhimmancin samun hadin kan Turai daidai yake da sake hadewar Jamus.
Mawallafa: Marcel Fürstenau / Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal