Bikin "ranar" Hausa
August 26, 2025
An yi a fadar maimartaba Sarkin Daura da ake wa lakabi da tushen Hausa an gudanar da nuna al'adun Hausa iri-iri domin kayata kuma taken bikin na bana shi ne amfani da harshen Hausa wajen wanzar da zaman lafiya. Abdulbaki Jari na daga cikin wadanda suke shirya bikin Kuma shi ne ya assasa bikin wannan rana ta kokarin ganin Majalisar Dunkin Duniya ta amince da ita.
Karin Bayani: Cece-kuce kan amfani da harshen Hausa a Jamhuriyar Nijar
Mahalarta taron sun yi Imani da cewa taron zai kara hada kan Hausawa a duk inda suke a cewar Kanal Muhammad Sani Masallaci Gwamnan jihar Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar wanda ya jagoranci tawagar kasar ta Nijar zuwa taron harshen Hausa na daga cikin abin da ya kara kula alakar kasashen biyu.
Duk da daukar shekaru goma ana wannan bikin na ranar Hausa har yanzu harshen na fuskantar kalubale abin da Wazirin Katsina Sanata Ibrahim Ida ke cewa akwai bukatar gudummuwar kowa da kowa. Makadan Hausa da mawaka da 'yan kokowa da wanzamai da makera duk sun bake kolin al'adunsu a wannan rana inda suka nishadantar da mahalarta taron.