Bayan shekaru 43, ko Biya zai magance matsalolin Kamaru?
July 14, 2025Shugaban Kamaru mai shekaru 92, Paul Biya da ya fi ko-wane shugaban kasa a duniya dadewa kan karagar mulki, ya ce zai nemi tazarce a zaben shugaban kasar da za a yi nan gaba a watan Oktoba domin ci gaba da nemo hanyoyin da zai gyara kasar.
Paul Biya ya ce: "na amsa kiraye-kirayen da dimbin jama'a suke yi min. Na amince zan tsaya a matsayin dan takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook cikin harshen Faransanci da kuma Turancin Ingilishi.
A halin yanzu Paul Biya ne shugaban kasa mai ci na biyu mafi dadewa a karagar mulki, bayan fara shugabantar Kamaru a shekarar 1982, wanda zuwa 2025 ya shafe shekaru 43 yana jagorantar kasar kuma shine shugaba mai tsufa kan karagar mulki a Duniya.
Ya sanar da takararsa bayan rattaba hannu a kan dokar zabe ranar Juma'a da ta gabata, wanda ke nuna cewa za a gudanar da zaben shugaban kasar ranar 12 ga watan Oktoba, kuma ranar Asabar da ta gabata aka kammala rajitar masu kada kuri'u yayin da kundin tsarin mulkin kasar ya ce kwanaki 90 bayan rattaba hannun shugaban kasa za a gudanar da zabe.
An daɗe ana tababa da nuna shakku dangane da shirin zaben da kuma takarar shugaba Biya, wanda ake bayyana cewar yawan shekaru da kuma rashin lafiya ka iya hana shi sake takara. Isma'ila Mohaman mai nazari ne a kan harkokin siyasa a Kamaru:
''Ka san da yawa daga cikin'yan Kamaru sun yi tsammanin cewa ganin yanayin tsufa na Paul Biya da kuma yadda al'amura suke gudana kusan ba a ganinsa a wasu ababe, a kan hake ne aka yi tsammani zai mika hannu zuwa ga dansa ko wanda kuma ake tsammanin kamar sakataren fadarsa, saboda ana ganin shi ne yake kusan gudanar da dukkan al'amura''.
Ali Dach dan siyasa na jam'iyyar adawa ta SDF: ''Zamu je zabe ko da kasancewar Biya ko ba da kasancewarsa ba, wannan ba zai iya sanyamu cikin damuwa ba, mun riga mun yi tanadi zamu tsaya takara tsarin da muka yi na tafiyar da Kamaru yana nan daban yake. Muna kira ga wasu jam'iyyun da mu hada gwiwa mu yi aiki tare,yanzu haka akwai wadanda suka fara nuna kai cikinsu har wadanda suka yi murabus daga gwamnatin Paul Biya''.
Mahaman Bello dan jam'iyyar RDPC mai mulkin kasar ya danganta sanarwar Paul Biya na tsayawa takatar zaben shugaban kasa da tarukan da sakataren fadar shugaban kasa ya jagoranta 'yan kwanakinan inda ya hada jiga-jigan jam'iyyar na ko wacce jiha domin sauraronsu:
''Idan Paul Biya ya tsaya yau nan, ina tsammanin cewa manyan magabatan jam'iyyarmu, sun duba cikin kwanakin da suka shude sakataren fadar shugaban kasa ya gayyaci dukkan yan majalisa da ministoci ya tattauna da su, ina ga cikin tattaunawar ne suka yanke shawarar ya kamata mai kasa ya sake tsayawa''.
Paul Biya cikinsakon nasa da ake wallafawa a shafinsa na Facebook, ya ce yana sane da tarin kalubalen da kasar ta Kamaru ke fuskanta, to amma yana neman hadin kan ‘yan kasar domin fuskantar matsalolin tare da magance su baki daya. Dokar zaɓen da Biya ya rattabawa hannu zata tilastawa dukannin masu sha'awar tsayawa takara, miƙa takardar buƙatar hakan ga hukumar zaɓe cikin kwanaki 10 masu zuwa.
Aƙalla 'yan siyasa sama da 20 suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar zaben shugaban ƙasa a Kamaru. Akwai 'yan adawa da wasu tsoffin ministocin Biya da suka dakatar da kawance da kuma wasu sabbin fuskoki daga bangaren ƙungiyoyin fararen hula.